25 Yuli 2020 - 10:13
An Cilla Rokoki Kan Wani Sansanin Sojojin ‘Yan Ta’adda Na Amurka A Kasar Iraqi

Kafafen yada labarai na kasar Iraqi sun bada sanarwan cewa an cilla makaman roka da dama kan sansanin sojojin Amurka da ke Basmayah kusa da birnin Bagdaza babban birnin kasar, inda sojojin Amurka da dama suke zaune.

ABNA24: Kamfanin dillancin labaran farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa hotunan da aka watsa na cikin sansanin sojojin na amurka ya nuna motocin kwan-kwana da dama suna kokarin kashe gobara a sansanin.

Har’ila yau wata majiyar tsaron kasar ta Iraqi ta bada sanarwan cewa makaman da aka cillan guda hudu ne kuma dukkaninsu samfurin katusha ne.

Ba’a bayyana irin asarorin da makaman suka haddasa a sansanin ba. Sai dai har yanzun majiyar ofishin jakadancin Amurka a Bagdaza ba ta fidda wani bayani dangane da wadannan hare-hare ba.

342/